Isa ga babban shafi

Peter Obi ya musanta labarin tsayawa takara a 2027

A Najeriya dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben shugaban kasa na 2023, Peter Obi, yayi watsi da rahotannin kafafen yada labarai na cewa yana fatan tsayawa takara a zaben shugaban kasa na 2027.

Peter Obi, dan takarar neman kujerar shugaban kasa na jam'iyyar Labour.
Peter Obi, dan takarar neman kujerar shugaban kasa na jam'iyyar Labour. AP - Mosa'ab Elshamy
Talla

Dan takarar shugaban kasar ya kuma musanta cewa yayi magana kan wadanda gwamnatin tarayya ta nada.

Peter Obi
Peter Obi © Daily Post
Peter Obi wanda kuma tsohon gwamnan Anambra ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Twitter a jiya  asabar a Legas.

Dan takarar shugaban kasar ya bayyana duka rahotannin biyu a matsayin na bogi, yana mai takaicin yadda siyasar Najeriya ta tabarbare har ta kai yadda ake amfani da kafafen yada labarai a halin yanzu .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.