Isa ga babban shafi

Gwamnonin Kudu maso Gabas da shugabannin Igbo na shirin ganawa da shugaba Tinubu

A Najeriya Gwamnonin Kudu maso Gabas da sauran shugabannin kabilar Igbo na shirin ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu kan matsalar rashin tsaro a yankunansu, Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ne ya sanar da haka a ranar alhamis.

Sabon shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu kenan.
Sabon shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu kenan. © premiumtimes
Talla

Gwamnan Hope Uzodinma na jihar Imo ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ganawarsa da Shugaban Najeriya Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Gwamnan ya tuna cewa shi da wasu gwamnonin jihohi biyar na Kudu maso Gabas da kuma shugabannin kungiyar al’adun kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo, sun yanke shawarar ganawa da shugaban kasar kan rashin tsaro a yankin.

Shugabanin Igbo a fadar Shugaban Najeriya ,zamanin Shugaba Buhari
Shugabanin Igbo a fadar Shugaban Najeriya ,zamanin Shugaba Buhari © Nigeria presidency

Ya bayyana cewa ya je fadar shugaban kasa ne domin samun ganawa da shugabannin yankin kudu maso gabas da Mista Tinubu.

“Ziyarar ta na da alaka da matsalar tsaro a kasar nan. Yankin Kudu-maso-gabashin kasar nan, ba shakka, kun san an yi ta fama da wannan babban matakin tsaro tun daga ‘yan fashi, da sace-sacen ‘yan bindigar da ba a san ko su waye ba,” inji shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.