Isa ga babban shafi

Amurka da kawayenta na shirin kafa rundunar rakiyar jiragen ruwa a tekun Maliya

Sakataren tsaron Amurka Lloyd Austin, da sanyin safiyar Talatar nan ya sanar da cewa Amurka da wasu da kawayenta na Shirin samar da wata sabuwar runduna da za ta kare jiragen ruwa da ke ratsa tekun Bahar Maliya da ke fuskantar hare-hare daga jiragen sama marasa matuka da makamai masu linzami da ake harbawa daga yankunan da Houthi na kasar Yemen ke iko da su.

Wani hari da mayakan Houthi na Yemen suka kai cikin wani jirgin ruwa a tekun bahar Maliya
Wani hari da mayakan Houthi na Yemen suka kai cikin wani jirgin ruwa a tekun bahar Maliya © Houthi militari media / via Reuters
Talla

Llord Austin ya bayyana hakan ne a ziyarar da yake yi a kasar Bahrain.

Munanan hare-haren, da mayakan Houthi da ke samun goyon bayan Iran ke kai wa domin matsayawa Isra’ila lamba don ta dakatar da kisan Falasdinawa, ya sa kamfanonin sufurin jiragen ruwa da dama sun sanar da dakatar da bin mashigin ruwan Bab el-Mandeb har sai an magance matsalar tsaro.

Babban jami’in na Amurka ya ce, Birtaniya da Bahrain da Canada da Faransa da Italiya da Netherlands da Norway da Seychelles da Spain za su bi sahun Amurka a cikin sabon rundunar tsaron tekun na Bahar Maliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.