Yakin Gaza: Amurka ta ce za ta ci gaba da taimaka wa Isra'ila da makamai
Amurka ta sha alwashin ci gaba da taimaka wa Isra’ila a yakin da taake da Hamas, a yayin da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ta dage kuri’ar da ta kudiri aniyar kadawa a game da rikicin Gaza.
Wallafawa ranar:
A yayin ziyarar da ya kai Isra’ila a Litinin din nan, sakataren tsaron Amurka, Lloyd Austin da ministan tsaron Isra’ila sun gudanar da wani taron manema labarai na hadin gwiwa, inda a nan ne ya yi kira ga karin agaji ga wadanda rikicin Gaza ya daidaita.
Sai dai Lloyd ya ce Amurka za ta ci gaba da samar wa Isra’ila taimakon kayan yaki don ci gaba da kokarin kakkabe mayakan Hamas, wanda suka ja daga tun bayaan harin 7 ga watan Octoba.
A waje daya kuma, majiyoyin diflomasiyya sun bayyana cewa an dage kuri’ar da aka tsara kadawa a game da rikicin Gaza a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zuwa wannan Talata, a yayin da ake ci gaba da tattauna abubuwan da daftarin da za a yi aiki da shi a yayin kuri’ar zai kunsa.
Ya zuwa yanzu, akalla mutane dubu 19 da dari 4 da 53 ne suka mutu tun da Isra’ila ta fara kai hare-hare zirin Gaza, kana, wadanda suka ji rauni sun kai dubu 52 da dari 2 da 86, a cewar mahukuntan Hamas.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu