Isa ga babban shafi

Mayakan Houthi sun sha alwashin hana jiragen ruwan daukar kaya shiga Isra'ila

Mayakan Houthi na Yemen sun sanar da shirin kaiwa manyan jiragen ruwan da ke kan hanyar su ta shiga Isra’ila hari ba tare da la‘akari da kasashen da suka fito ba, yayin da suka gargadi kasashen duniya da kamfanoni da su guji kulla wata harkar kasuwanci da Isra’ila a halin yanzu, musamman wadda zata shafi zirga-zirgar ruwa.

Mayakan sun ce ba zasu dakatar da wannan kuduri nasu ba har sai an bada damar shigar da kayan agaji Gaza
Mayakan sun ce ba zasu dakatar da wannan kuduri nasu ba har sai an bada damar shigar da kayan agaji Gaza via REUTERS - LEHTIKUVA
Talla

Ta cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce matukar ba za’a baiwa kayayyakin agaji da na abinci damar shiga Gaza ba, to kuwa tabbas babu abinda zai kara shiga Isra’ila ta tekun Bahar maliya.

Wannan sanarwa na kara fito da barzanar da ake da ita na yaduwar wannan yaki zuwa kasashen Gabas ta tsakiya.

Bayanai na nuna cewa a baya-bayan nan mayakan na Houthi da ke samun goyon bayan Iran sun kwace manyan jiragen ruwa makare da kaya wadanda ke kan hanyar su ta isa Isra’ila.

Mayakan na Houthi sun ce sun dauki wannan mataki ne  don nuna goyon bayan su ga Palasdinawa, sai dai kuma Isra’ila ta ce hare-haren da mayakan ke kaiwa jiragen ta, wani bangare ne na abinda ta kira “ta’addancin Iran” yayin da ta sha alwashin daukar mataki.

Tuni dai kasashen Amurka da Burtaniya suka yi Allah wadai da hare-haren kan jiragen da ke shirin shiga Isra’ila, yayin da suka zargi Iran da taka rawa a wannan danyen aiki, sai dai kuma Iran din ta musanta hannu, tana mai cewa matakin shawarar Houthi ce zalla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.