Isa ga babban shafi
RIKICIN GAZA

Hamas ta dakatar da duk wata tattaunawa da Isra'ila

A ranar Laraba,  sojojin Isra'ila sun yi wa yankin kudancin birnin Gaza kawanya, inda suke fafatawa da mayakan Hamas a wani kazamin fada da aka kwashe watanni biyu ana gwabzawa.Rikicin ya koma kudancin yankin da aka yi wa kawanya, biyo bayan kazamin fada da tashin bama-bamai  da ya rutsa da yankin arewacin Falesdinu, tare da tilastawa mutane kusan miliyan biyu barin gidajensu.

Shugaban kungiyar Hamas  Ismail Haniya na gaisuwa lokacin da ya isa Gaza a ranar 16 ga watan December 2018  a lokacin bikin cika shekaru 31 da kafa kungiyar mai ra'ayin musulunci dake gwagwarmaya da makamai wajen nemar wa falestinawa yancin kai
Shugaban kungiyar Hamas Ismail Haniya na gaisuwa lokacin da ya isa Gaza a ranar 16 ga watan December 2018 a lokacin bikin cika shekaru 31 da kafa kungiyar mai ra'ayin musulunci dake gwagwarmaya da makamai wajen nemar wa falestinawa yancin kai AFP
Talla

Isra'ila ta ce, dakarunta sun kutsa kai a sansanin yan gudun hijira na  Khan Younis da ke kudancin yankin Gaza,  tare da yi masa  ruwan bama-bamai a cikin daren talata .

Rundunar  sojin, ta ce ta kai hari ne, a sansanin 'yan gudun hijirar Jabaliya da ke arewacin Gaza.

Jami’in kungiyar Hamas, Osama Hamdan, ya sanar da  wani taron manema labarai cewa, babu batun shiga wata tattaunawa ko yin wata  musayar fursunoni ba, har sai an daina kai hare haren  da Isra’ila ke yi  kan Gaza.

Sojojin Isra'ila sun umarci Falasdinawa da ke  Khan Younis da su kauracewa sansanin zuwa yankin yammancin gabar yammacin kogin Jordan zuwa kudancin  Rafah dake daf da iyakar kasar  Masar.

Kungiyoyin agaji sun yi gargadin cewa, al'ummar Gaza na ci gaba da tserewa wuraren matsuguninsu, a yayin da yawan mutanen da suka rasa matsuguninsu su kai haura miliyan 1.9, in ji  Majalisar Dinkin Duniya.

Idan dai ba a manta ba a ranar 7 ga watan oktoban da ya gabata ne Kungiyar mayakan Hamas ta kai wani mummunan hari a kudancin Isra'ila, inda ta kashe  yahudawa sama da 1,200, tare da yin garkuwa da kusan 240, a cewar gwamnatin Isra'ila.

Tun daga wannan lokaci dai ne kawo yanzu, akalla adadin mutane dubu 16,248 da suka hada da kananan yara 7,112 ne Isara’ila ta kashe a zirin na Gaza, a cewar ofishin kiyon lafiyar gwamnatin Hamas.

A yayin da a jimilce kimanin mutane  dubu 43,616 ne suka jikkata, kuma akalla wasu mutanen da yawansu ya kai dubu  7,600 sun bata, in ji ofishin yada labaran Hamas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.