Sama da Falasdinawa dari 7 hare-haren Isra'ila ya kashe a karshen mako
Daruruwan Falasdinawa sun rasa rayukansu a karshen mako, sakamako hare-haren sojojin Isra’ila a yankin Gaza, musamman kan birnin Khan Younis.
Wallafawa ranar:
A baya dai kasashen Qatar da Masar sun samu nasarar shiga tsakani wajen kulla yarjejeniyar tsagaita wuta, wacce ta fara aiki a ranar 24 ga watan daya gabata.
Tsagaita wutar da ta bada damar musayar fursunini a tsakanin bangarorin Isra’ila da Hamas, sau biyu a na tsawaitata, sai dai a ranar Juma’ar da ta gabata ne ta kawo karshe.
Kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wutar, hare-haren Isra’ila ta sama da kuma kasa sun yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa dubu 14, yawancinsu mata da kananan yara ne, sannan kimanin mutane miliyan daya da dubu dari 7 suka tsere daga gidajensu.
Daraktan yada labaran gwamnatin Gaza Ismail Al-Thawabta, ya shaidawa kafar Al Jazeera cewa sama da Falasdinawa dari 7 ne aka kashe a cikin sa’o I 24 da sake faro rikicin.
An dai bada rahoton ci gaba da ruwan bama-bamai da Isra'ila ke yi a yankunan Khan Younis da Rafah da kuma wasu bangarorin yankin Arewacin Gaza da ake zargin sojojin Isra’ila na kai wa hare-hare cikinsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu