Isa ga babban shafi

Isra'ila ta ci gaba da ruwan bama-bamai a Gaza

A rana ta biyu bayan karewar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas, Isra’ila ta ci gaba da ruwan bama-bamai a yankin Gaza, bayan da aka gaza cimma wata yarjejeniyar duk kuwa da bukatar hakan da kasashen duniya suka gabatar.

Yadda hayaki ya turnuke sararin samaniyar yankin Arewacin Gaza, bayan wani hari da Isra'ila ta kai.
Yadda hayaki ya turnuke sararin samaniyar yankin Arewacin Gaza, bayan wani hari da Isra'ila ta kai. REUTERS - AMIR COHEN
Talla

Kakakin rundunar tsaron Isra'ila Jonathan Conricus ya shaidawa manema labarai a yau Asabar cewar suna kaiwa Hamas hari ne.

"Abin da muke yi yanzu shi ne kai farmaki kan mayakan Hamas a duk fadin zirin Gaza."

Ma’aikatar kula da lafiyar yankin Falasdinu, ta ce tun bayan kaddamar da sabbin hare-hare da Isra’ila ta yi a yankin Gaza a jiya Juma’a, kimanin mutane dari 2 ne suka rasa rayukansu.

Wasu daga cikin mutanen da suka samu raunuka sanadiyar hare-haren Isra'ila.
Wasu daga cikin mutanen da suka samu raunuka sanadiyar hare-haren Isra'ila. AP - Fatima Shbair

Bangarorin biyu dai na zargin juna da gazawa wajen tsawaita yarjejeniyar tsawaita wuta, inda Isra’ila ta yi ikirarin cewar Hamas ta yi yunkurin kai mata hari rokoki a lokacin da aka tsagaita wuta da kuma gazawarta wajen fidda sunayen sauran mutanen da take rike dasu.

Fara ministan Belgium Alexandre De Croo ya shaidawa manema labarai a wajen Yanayi na duniya COP28 da ke gudana a Dubai cewar, sun tattauna da takwaransa na Isra’ila Benjamin Netanyahu, kan kawo karshen kashe fararen hula a yakin.

Ya kuma ce suna fatan ci gaba da amfani da iyakar Rafah, wacce ta kasance a rufe tun bayan sake kaddamar da hare-haren da Isra'ila ta yi, don kai kayan agaji yankin na Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.