Isa ga babban shafi

Yaduwar cutuka a Gaza za ta fi hare-haren Isra'ila muni - WHO

Hukumar lafiya ta duniya WHO, za a samu mutuwar mutane da dama, fiye da wadanda suka mutu a sakamakon ruwan bamabaman da Isra’ila ta harba a Gaza, saboda tarnakin da wadannan hare-hare suka haifar ga bangaren lafiya.

Wasu daga cikin Falasdinawan da harin Isra'ila ya shafa, yayin da suke karbar kulawa a asibitin Al Shifa.
Wasu daga cikin Falasdinawan da harin Isra'ila ya shafa, yayin da suke karbar kulawa a asibitin Al Shifa. © STRINGER / Reuters
Talla

Mai Magana da yawun hukumar, Margaret Harris, za a samu bullar cutuka da dama a Gaza, saboda matsalolin da suka mamaye sha’anin kiwon lafiya, idan har hukumomi basu dauki matakan gaggawa ba.

Ta bayyana rushe asibitin Al Shifa da ke arewacin Gaza, a matsayin ibtila’I mafi muni da aka gani a tarihi, inda ta nuna damuwa kan tsare wasu daga cikin jami’an lafiya da sojojin Isra’ila suka yi.

Motocin agaji 200 suka isa arewacin Gaza tun bayan da aka cimma yarjejeniya tsakanin Isra’ila da Hamas a makon jiya, kamar yadda kungiyar agaji ta falasdinu ta sanar.

Bayan tsawaita wannan yarjejeniya, ana sa ran Hamas zata sako wasu daga cikin mutanen da take tsare da su, domin musayar Falasdinawan da ke gidajen yarin Isra’ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.