Isa ga babban shafi

Duk da tsagaita wuta a yankin Gaza, Isra'ila ta ci gaba da kai hari

Isra'ila da Hamas sun amince da yarjejeniyar da Qatar ta shiga tsakaninta na tsagaita wutar kwanaki hudu a Gaza da kuma sakin fursunoni 50 da ake tsare da su a yankin tun bayan harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba. 

Yadda Isra'ila ke ruwan bama-bamai a Gaza. 22/11/23
Yadda Isra'ila ke ruwan bama-bamai a Gaza. 22/11/23 AP - Leo Correa
Talla

Sakin kimanin mata da yara kanana Falasdinawa 150 da ake tsare da su a gidajen yarin Isra'ila na wani bangare na yarjejeniyar.

Isra'ila zata jinkirta musaya

Kafofin yada labaran Isra'ila sun ce ana sa ran sakin  farko na mutanen da akayi gurkuwa da su a wannan Alhamis, in da Isra’ila a bangarenta zata jinkirta aiwatar da yarjejeniyar har tsawon sa'o'i 24 don bai wa yahudawa damar neman kotun kolin ta hana sakin fursunonin Falasdinu da ke tsare.

Qatar

Babban mai shiga tsakani na Qatar a tattaunawar tsagaita wuta, karamin ministan harkokin wajen kasar Mohammed Al-Khulaifi, ya tabbatar da cewa kungiyar agaji ta Red Cross za ta yi aiki a cikin Gaza domin samun saukin sako mutanen da aka yi garkuwa da su.

Hotunan wasu mata akasari Yahudawa da Hamas ta tsare bayan harin da ta kai Isra'ila ranar 7 ga wata Oktoba 22/11/23
Hotunan wasu mata akasari Yahudawa da Hamas ta tsare bayan harin da ta kai Isra'ila ranar 7 ga wata Oktoba 22/11/23 AP - Oded Balilty

Yayin da gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden ke fatan tsagaita wuta a Gaza ta kai ga dakatar da fada a kan iyakar Isra'ila da Lebanon, kamar yadda wani babban jami'in Amurka ya bayyana da yammacin Talata.

Ci gaba da kai hari Gaza

Tun cikin dare da wayewar garin wannan Alhmis sojojin Isra'ila sun kara ci gaba da kai hare-hare a yankin zirin Gaza, saboda dama ta ce yarjejiyar bazata hana ta ci gaba da kai hari ba.

An kai harin bam a wata gona a Khan Younis, kuma an kai hari kan sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat inda aka kashe Falasdinawa da dama.

A arewacin kasar an kai hari a yankunan da ke kusa da asibitin Indonesiya da kuma asibitin Kamal Adwan, yayin da rahotanni sukace an harbi motar daukar marasa lafiya.

Hakazalika an kai harin bam a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia, wanda a baya sojojin Isra'ila suka sha kaddamar da farmaki

Fiye da Falasdinawa 2,000 aka bada rahoton bacewarsu a karkashin baraguzan gine-gine, inda kungiyoyin kare fararen hula ke fuskantar babbar matsala wajen kubutar da su.

Baza mu bar sojojin Isra'ila ba - Islamic Jihad

Kungiyar Islamic Jihad ta Falasdinu ta ce ba za a saki fursunonin Isra'ila da ba farar hula ba ne.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin Telegram, kungiyar Islamic Jihad  ta Falasdinu (PIJ) ta ce ba za a saki sojojin Isra'ila ba har sai "dukkan fursunoninsu dake gidajen yarin abokan gaba sun samu 'yanci.

Baya ga Hamas, kungiyar ta PIJ ta tsare wadanda ta kama daga Isra'ila tun ranar 7 ga watan Oktoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.