Isa ga babban shafi

Isra'ila za ta tsagaita luguden wuta a Gaza daga gobe

Yarjejeniyar tsagaita musayar wuta tsakanin Isra’ila da Hamas za ta fara aiki a gobe Juma’a da misalin karfe 7 na safe agogon Gaza kamar yadda gwamnatin Qatar da ke shiga tsakani ta bayyana.

Wani harin roka a yakin Gaza.
Wani harin roka a yakin Gaza. AP - Tsafrir Abayov
Talla

Tsagaita bude wutar za ta fara ne da zaran Hamas ta saki wasu Yahudawa da take garkuwa da su da suka hada da mata da kananan yara, kuma hakan na zuwa ne bayan shafe tsawon makwanni shida ana dauki-ba-dadi.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Qatar , Dr. Majed al Ansari ya ce, sun karbi jerin sunayen mutanen da za a fara sakin su da misalin karfe 4 na asuba a gobe Juma’ar, yayin da ake sa ran Isra’ila  ita ma ta saki Falasdinawan da ta garkame a gidan yari.

Sojojin Isra'ila a Gaza.
Sojojin Isra'ila a Gaza. © IDF

Kodayake yarjejeniyar tsagaita bude wutar ta wucin-gadi ce, amma ana sa ran za ta yi tasiri ta yadda za a kai ga kulla yarjejeniyar tsagaita wutar ta din-din-din a Zirin Gaza da yaki ya daidaita.

 

Gwamnatin Qatar na fatan cewa, ba za a sake samun jinkirin cimma yarjejeniyar ba, ganin cewa komai ya kammalu a yanzu.

Wannan yarjejeniyar dai, za ta bada damar  shigar da daruruwan motoci dauke da kayan agaji da suka hada da magunguna da man fetur cikin Gaza, inda kuma Isra’ila za ta kawo karshen luguden wutarta ta sama a yankin kudancin Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.