Isa ga babban shafi
YAKIN ISRA'ILA DA HAMAS

Hamas ta sako rukunin farko na mutanen da ta kama

Majiyoyin Hamas biyu sun tabbatar da mika fursunonin da ke hannunsu ga kungiyar agaji ta Red Cross domin mayar da su Isra’ila ta kasar Masar.

Yadda wasu 'yan 'uwa ke murnar sako fursunonin da Hamas ta kama.
Yadda wasu 'yan 'uwa ke murnar sako fursunonin da Hamas ta kama. AP - Ariel Schalit
Talla

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa, kungiyar agajin ce za ta isar da fursunonin zuwa Isra’ila ta mashigar Rafah da ke Masar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, Yahudawa 24 Hamas ta bawa yancin zuwa gida, daga cikin wadanda ta yi garkuwa da su ya zuwa yanzu.

Wata majiyar rundunar sojin Hamas, wadda ta tabbatar da sakin wasu daga cikin fursunoni, ta ce wannan shine kaso na farko, karkashin yarjejeniyar da aka kulla.

Wani faifan bidiyo ya nuna yadda iyalan wasu daga cikin Falsdinawan da ke tsare a hannun Isra’ila, wadanda ke jiran isowar ‘yan ‘uwansu a Yammacin Gabar Kogin Jordan.

Akalla Falasdinawa 39 ne cikin har da yara kanana da kuma mata ake sa ran Isra’ila z ata sako karkashin yarjejeniyar da ta kulla da wakilan Hamas.

Bayan makonni bakwai Isra'ila na barin wuta a Gaza, yanzu haka iyalai da dama na cike da farin cikin tarbar 'yan 'uwansu da ke daure.

Isra'ila dai ta ce, an haramta shiga arewacin Gaza, yayin da 'yan gudun hijirar Falasdinu ke kokarin komawa yankin nasu, sakamakon dakatar da kai hare-haren da aka samu.

Sama da Falasdinawa 14,000 aka kashe a Gaza, tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba, yayin da a Isra'ila, mutum 1,200 ne aka tabbatar harin Hamas ya kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.