Isa ga babban shafi
RIKICIN ISRA'ILA DA HAMAS

Masu shiga tsakani na tattaunawa kan yuwuwar tsagaita wuta a Gaza

Isra’ila da Hamas na tattaunawa kan yadda za a tsawaita tsagaita batun bude wuta a Gaza, inda masu shiga tsakani ke fafutukar yadda za a cimma matsaya, sa’o’i kalilan suka rage wa’adin yarjejeniyar da aka kulla ya kare.

Wata mace tare da karenta da Hamas ta sako, yayin musayar fursunoni a ranar 28 ga Nuwamba, 2023.
Wata mace tare da karenta da Hamas ta sako, yayin musayar fursunoni a ranar 28 ga Nuwamba, 2023. © Al-Qassam Brigades, Military Win / Reuters
Talla

Masu shiga tsakani dai na fatan za a tsawaita wannan yarjejeniya har zuwa tsawon kwanaki biyu, kamar yadda majiyoyin tsaron Masar suka sanar.

Har yanzu dai ana tattaunawa kan yadda za a sako sauran farern hular da ke hannun Hamas.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken y ace, za su yi dukkan mai yuwuwa don ganin an tsawaita wannan yarjejeniya, tare da kawo karshen yakin, yayin wata ziyara da ya kasai Isra’ila.

Isra’ila dai ta ce ta karbi cikakkun bayani kan wadanda take kyautata zaton Hamas za ta sako su a ranar Laraba.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce za a gudanar da cikakken bincike, kan rahoton da ke cewa Hamas ta ci zarafin wadanda ta cafke a ranar 7 ga watan Oktoba.

An kasha mutane biyu, yayin wani samame da dakarun Isra’ila suka kai garin Jenin da ke Yammacin Gabar Kogin Jordan a ranar Laraba, a cewar sanarwar da hukumomin Falasdinu suka fitar.

A ranar Litinin din makon jiya ne, Isra’ila da Hamas suka cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta tsawon kwanaki biyu.

Tun daga ranar Juma’a, Hamas ta sako Yahudawa 81 domin musayar Falasdinawa 180 da ke tsare a gidajen yarin Isra’ila.

A ranar 7 ga watan Oktoba ne, Hamas ta kai hari kudancin Isra’ila, tare da kashe mutum 1,200, inda ta yi garkuwa da mutum 240, a cewar sanarwar gwamnatin Isra’ila.

Tun daga lokacin, Isra’ila ta fara kaddamar da hari a Zirin Gaza, abin da ya yi sanadin rayukan Falasdinawa 14, 500, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta Hamas ta tabbatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.