Isra'ila da Hamas sun amince da tsawaita yarjejeniyarsu da karin kwana 2
An ci gaba da musayar fursunoni tsakanin Isra’ila da Hamas bayan tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar da ke tsakaninsu, matakin da ke zuwa bayan shiga tsakanin Qatar a wani yunkuri na samar da sassauci a yakin na fiye da wata guda.
Wallafawa ranar:
An yi nasarar tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar ne sa’o’i kalilan gabanin kawo karshen yarjejeniyar farkon haka zalika jim kadan bayan sakin wasu fursunoni 11 da Hamas ta yi wanda ya kai ga sakin Falasdinawa 33 daga gidan yarin Isra’ila.
Bayan kara wannan wa’adi na yarjejeniyar, Hamas ta sake sakin fursunonin 20 wanda ya kai ga sakin Falasdinawa 60 daga gidan yarin Isra’ila galibinsu mata da kananan yara kamar yadda yarjejeniyar ta kunsa.
Tuni shugaba Emmanuel Macron ya yi maraba da sakin fursunonin Faransa karkashin yarjejeniyar tsawaita shirin tsagaita wutar.
A bangare guda Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin ci gaba da luguden wuta a Gaza da zarar yarjejeniyar tsagaita wutar ta kawo karshe.
Tuni wani jirgin yakin Masar makare da kayakin agajin asibiti ya isa iyakar gaza don bayar da kulawa ga tarin fararen hular da Isra’ila ta jikkata.
Daga ranar 7 ga watan Oktoba zuwa yanzu Isra’ila ta kashe Falasdinawan da yawansu ya haura dubu 14 da 500 baya ga jikkata dubbunan daruruwa galibinsu mata da kananan yara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu