Isa ga babban shafi

Isra'ila ta mika wa Hamas Falasdinawa 39 da ta ke tsare da su

An shiga kwana ta uku a kwarya -kwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da mayakan Hamas na yankin Falasdinawa a Lahadin nan, inda ma’aikatar tsaron Isra’ila ta ce Hamas ta mika wa kungiyar agaji ta Red Cross jimillar mutane 17 daga cikin wadanda take garkuwa da su.

Daya daga cikin wadanda Hamas ta mika wa Isra'ila a cci gaba da mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki hudu da suka kullla.
Daya daga cikin wadanda Hamas ta mika wa Isra'ila a cci gaba da mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki hudu da suka kullla. via REUTERS - ISRAEL DEFENSE FORCES
Talla

Biyo bayan haka ne Isra’ila ta  saki kimanin Falasdinawa 39 daga cikin wadanda ta garkame a gidajen yarinta, a wani mataki na mutunta yarjejeniyar da suka cimma.

Tun  da farko a ranar Asabar da ta gabata, an samu tsaiko da jinkiri wajen ci gaba da aiwatar da tanade-tanaden yarjejeniyar, bayan da mayakan Hamas ta zargi Isra’ila da rashin mutunta wani bangare na yarjejeniyar, ta wajen dakile yawan motocin dakon kayan agaji da za su shiga Gaza, abin da Hamas ta ce ba zai  yiwu ba.

Hakan ne ma ya sa kasashen Qatar da Masar suka shiga tsakani, har suka gyara lamarin.

A ranar 7 ga watan Oktoba ce yaki ya barke tsakanin Isra’ila da Hamas, biyo bayan harin da Hamas din ta shammace ta da shi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane dubu 1 da dari 4.

Martanin da Isra’ila ta mayar ne ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da dubu 14, akasari fararen hula da suka hada da mata da yara, lamarin da ya janyo caccaka daga sassan duniya.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.