Isa ga babban shafi

Majalisar dokokin Afirka ta Kudu ta amince da katse hulda da Isra'ila kan Gaza

Majalisar dokokin Afirka ta Kudu ta kada kuri’ar amincewa da kudirin neman rufe ofishin jakadancin Isra’ila da ke Pretoria tare da dakatar da huldar diflomasiyya da kasar  yayin da takun saka tsakanin kasashen biyu kan hare-haren Isra’ila a Gaza ke kara tsananta.

Shugaban kasar Afrika ta Kudu Syril Ramaphosa yayin taron kasashen BRICS ta hoton bidiyo.21/11/23
Shugaban kasar Afrika ta Kudu Syril Ramaphosa yayin taron kasashen BRICS ta hoton bidiyo.21/11/23 AP
Talla

Kudirin na ranar Talata da ya bukaci a rufe ofishin jakadancin da kuma dakatar da duk wata huldar diflomasiyya har sai an cimma matsayar tsagaita wuta a Gaza, ya samu amincewa da gagarumin rinjayen kuri'u 248 kan 91 da suka ki amincewa.

Jam'iyyar adawa ta Economic Freedom Fighters ce ta gabatar da kudirin, wanda ke samun goyon bayan jam'iyyar African National Congress mai Mulki, da kuma adawar masu ra'ayin rikau, akasari fararen fata, masu goyon bayan Isra'ila ta Democratic Alliance.

Shugaba Ramaphosa

Shugaban Syril Ramaphosa ya ce kasarsa ta yi amanna cewa Isra'ila na aikata laifukan yaki da kisan kiyashi a yankin Zirin Gaza da aka yi wa kawanya, inda mahukuntan Falasdinu suka ce sama da mutane 14,100 ne aka kashe a hare-hare ta sama da ta kasa da Isra'ila ta kai tun ranar 7 ga watan Oktoba.

Yakin Gaza na baya-bayan nan ya samo asali ne a lokacin da kungiyar Falasdinawa dauke da makamai ta Hamas ta kai wani harin ba-zata a kudancin Isra'ila wanda mahukunta a can suka ce ya kashe mutane kusan 1,200.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.