Isa ga babban shafi

Kotun Afrika ta Kudu ta hana gwamnati korar 'yan Zimbabwe

A hukuncin da wata kotun Afirka ta Kudu ta yanke, ta umarci gwamnatin kasar da ta sake duba matakin da ta dauka na soke takardar izinin zama da ta bai wa kimanin ‘yan Zimbabwe dubu 200 da ke zaune kuma suke aiki a kasar. 

Shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa.
Shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa. © ©CyrilRamaphosa
Talla

 

Matakin na gwamnatin Afrika ta Kudu zai tilasta wa ‘yan Zimbabwe da ke zaune a kasar ba tare da cikakkun takardun aiki ba komawa kasarsu ta asali, koda kuwa suna da ‘ya’yan da suka haifa a kasar da ke zaman ‘ya’yanta. 

Sai dai a hukuncin da babbar kotun Gauteng da ke Pretoria ta yanke ta ce, matakin da ma’aikatar kula da harkokin cikin gida ta kasar ta dauka a shekarar da ta gabata kan ‘yan Zimbabwe da ke zaune a kasar ya saba wa doka domin ba’a bi ka’idar da ta kamata ba wajen daukar sa. 

A baya dai ma’aikatar ta tsayar da ranar 30 ga wannan watan a matsayin ranar da dokar za ta fara aiki, amma sai dai yanzu a karkashin hukuncin na kotun, an tsawaitata har zuwa ranar 28 ga watan Yunin shekara mai zuwa. 

Gidauniyar Helen Suzman da kuma kungiyoyin da ke kare hakkin ‘yan cirani a Afrika ta Kudu suka shigar da karar ma’aikatar kula da harkokin cikin gida ta kasar don kalubalantar wannan matakin da ta dauka. 

Akwai kimanin ‘yan kasar Zimbabwe dubu 100 da 78 da ke zaune a kasar Afrika ta Kudu a karkashin tsarin da aka samar a shekarar 2010 a kokarin kula da ‘yan ciranin Zimbabwe da ke guje wa matsalar tattalin arzikin kasarsu.   

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.