Isa ga babban shafi

Ana fargabar ambaliyar ruwa na iya kara tsanata a Kenya

Kenya na fama da ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda ya kawo cikas ga harkokin kasuwanci na yau da kullum a fadin kasar, abin da kuma hukumomi suka ce ya janyo asarar dukiya da rayukan mutum 44 kawo yanzu.

Wuraren da wannan ambaliya tafi yiwa barna sun hada da birnin Mombasa da kuma Malindi, hadi da yankunan da ke arewacin kasar masu iyaka da Somalia.
Wuraren da wannan ambaliya tafi yiwa barna sun hada da birnin Mombasa da kuma Malindi, hadi da yankunan da ke arewacin kasar masu iyaka da Somalia. © TheWeather
Talla

Kungiyar agajin kasar ta Red Cross, ta ce mamakon ruwan saman ya shafi rayuwar mutane kusan 60,000.

A cikin unguwar Mathare da ke Nairobi, babban birnin kasar, mazauna wurin da galibinsu masu karamin karfi ne, sun tsinci kansu makale a cikin gidajensu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa a ranar Larabar da ta gabata biyo bayan ruwan sama da aka kwashe tsawon dare ana zabgawa.

Hukumomin kasar sun fitar da sanarwar cewa, an dakatar da ayyukan layin dogo, sannan an rufe wasu manyan tituna na wucin gadi, sakamakon ibtila’in da aka shiga.

Ma'aikatar hasashen yanayi ta Kenya ta yi hasashen cewa za a ci gaba da samun ruwan sama a yankuna daban-daban na kasar, wanda ake fargabar zai iya haifar da ambaliya mai munin gaske.

Gwamnatin Kenya ta sanar da cewa an kara daukar matakan gaggawa domin tunkarar ambaliyar ruwan a sassa daban-daban na kasar sakamakon mamakon ruwan sama da ake ci gaba da yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.