Isa ga babban shafi

Masu bore a Tunisia sun bukaci a kori bakin haure daga sansaninsu

A yau asabar dubban 'yan Tunisiya ne suka gudanar da zanga-zanga a garin El Amra domin nuna adawa da sansanonin wucin gadi na bakin haure daga kasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara.

Wani sansanin yan cin rani a harabar hukumar bakin haure ta MDD  a Tunis
Wani sansanin yan cin rani a harabar hukumar bakin haure ta MDD a Tunis AP - Hassene Dridi
Talla

Rahotanni daga yanki na nunin cewa jama’a sun taru ne a wani karamin gari da ke tsakiyar kasar Tunusia biyo bayan matakin da hukumomi suka dauka a baya-bayan nan kan sansanonin da aka yi a Tunis babban birnin kasar da ma wasu yankuna, bayan korafe-korafen mazauna yankin.

A El Amra, masu zanga-zangar sun yi kira da a “fice”da  bakin haure cikin “sauri”.

Wasu daga cikin bakin haure a Sfax
Wasu daga cikin bakin haure a Sfax © Amira Souilem/RFI

Wani dan majalisa mai suna Tarek Mahdi ya ce "mafita cikin gaggawa" kamata 'yan ci-rani su bar biranen ba tare da bata lokaci ba.

Lamarin ya zama abin da ba za a amince da shi ba, kuma dole ne hukumomi su samar da mafita, in ji wannan dan majalisa , wanda ke wakiltar El Amra a majalisar dokokin kasar.

Migrants wait to be transferred from Lampedusa Island, Italy, Sept. 15, 2023.
Bakin haure a Lampedusa AP - Valeria Ferraro

Ya kara da cewa ya kamata sauran kasashe su taimaka wa Tunisia wajen tunkarar matsalar kwararar bakin haure.

Garin yana da tazarar kilomita 40  arewa da Sfax, daya daga cikin hanyoyin da bakin haure ke amfanin da ita wajen tsallakawa Turai ta hanyar teku.

Bakin haure da dama sun yi gudun hijira zuwa garuruwa irin su El Amra, inda suka kafa sansani kafin su tsallaka tekun Mediterrenean mai cike da hadari, yayin da hukumomin Tunisia da kungiyar Tarayyar Turai suka kara kaimi wajen dakile kwararar bakin haure.

Wasu daga ciknin yan cin rani a sansanin bakin haure
Wasu daga ciknin yan cin rani a sansanin bakin haure AFP - IMED HADDAD

An samu karuwar tashe-tashen hankula na kyamar bakin haure a bara, biyo bayan kalaman da shugaba Kais Saied ya yi wanda ya zana ‘yan kasashen waje “ba bisa doka ba” a matsayin barazana ga al’umma, ya kuma kori da yawa daga manyan biranen kasar zuwa kananan garuruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.