Isa ga babban shafi

'Yan cirani 21 sun mutu wasu 23 sun bace yayin tsallakawa Saudiya ta Djibouti

Hukumar kula da kaurar baki ta Majalisar Dinkin Duniya IOM ta ce ‘yan cirani 21 suka mutu yayinda wasu 23 suka bace bayan nutsewar jirgin da ke dauke da su a gabar ruwan Djibouti, a hadarin da ke matsayin irinsa na biyu cikin makwanni biyu.

Wasu 'yan ciranin Afrika.
Wasu 'yan ciranin Afrika. © Borja Suarez/Reuters
Talla

Sanarwar ta IOM na zuwa ne a dai dai lokacin da mahukuntan Tunisia ke sanar da tsamo gawarwakin ‘yan cirani 19 daga gabar ruwan kasar wadanda suka kama hanyar isa tsibirin Lampedusa na Italiya, adadin da ya mayar da ‘yan ciranin da suka mutu a wannan hanya zuwa kusan 200 a watanni 4 na shekarar nan.

Sakon da IOM ta wallafa a shafinta na X ya bayyana cewa jirgin ‘yan ciranin ya bar Djibouti dauke da mutane 77 gabanin nutsewa a tsakar teku inda aka tsamo gawarwakin mutane 21 ciki har da kananan yara 16 a bangare guda kuma ake neman wasu 23 da suka bace.

Dubban daruruwan ‘yan ciranin kasashen kuryar gabashin Afrika galibi daga Habasha da Somalia ne ke ratsa gabar ruwan ta Djibouti a kokarin isa Saudi Arabia da kasashen yankin Gulf da nufin samun ayyukan dogaro da kai, lamarin da a wasu lokutan kan kai ga asarar rayukansu.

A cewar IOM galibin ‘yan ciranin kan makale a Yemen inda suke rayuwa cikin tsananin tagayyara da wahalhalu iri-iri, yayinda kaso mai yawa kan nutse a ruwa tun gabanin isa inda suka nufa.

A cewar Ofishin IOM na Djibouti, an yi nasarar ceto wasu mutum 33 daga ruwan kuma dukkanin wadanda suka mutu sun fito ne daga Habasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.