Isa ga babban shafi

Juyin mulkin Soji a Nijar ya ta'azzara yanayin kwararar baki zuwa Turai- EU

Hukumar kula da ‘yan cirani ta kungiyar tarayyar Turai ta yi gargadin yiwuwar juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar cikin shekarar da ta gabata, ya iya haifar da karuwar kwararar bakin haure zuwa nahiyar.

Migrants wait to be transferred from Lampedusa Island, Italy, Sept. 15, 2023.
Wasu tarin bakin haure a tsibirin Lampedusa na Italiya. AP - Valeria Ferraro
Talla

Kwamishiniyar harkokin cikin gidan kungiyar Ylva Johansson, ta ce dole ne kungiyar ta dauki matakai don kange yawaitar kwararar bakin zuwa nahiyar wanda kaso mai yawa ke bin saharar Nijar gabanin isa bakin teku.

Nijar na matsayin babbar hanyar da ‘yanciranin yankin saharar Afrika kan yi amfani da ita wajen shiga Turai, kuma tun bayan juyin mulkin sojojin da ke jagoranci a kasar suka janye daga wata yarjejeniya tsakaninsu da EU da ta basu damar kange bakin da ke shiga Turai ta sahara, wanda ya sanya ganin turuwar masu wannan balaguro.

Wasu alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewar, sama da mutane dubu 45 da dari 5 ne suka tsallaka nahiyar ta haramtacciyar hanya a wannan shekarar kadai, duk da dai adadin bai kai na shekarar 2015 ba, inda sama da mutane miliyan daya yawancinsu ‘yan gudun hijirar Syria ne suka shiga Turai.

Tun daga lokacin ne kuma kasashe 27 mambobin kungiyar suka matsa kaimi wajen rage yawan kwararar bakin haure daga yankin gabas ta tsakiya da kuma Afrika, ta hanyar tsaurara tsaro a iyakoki da kuma dokokin neman mafaka a nahiyar baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.