Zanga-zangar neman ficewar sojojin Amurka daga arewacin Nijar
Dubban jama'a a Jamhuriyar Nijar sun gudanar da zanga-zangar neman ficewar sojojin Amurka daga arewacin kasar a jiya Asabar, bayan da gwamnatin mulkin soja a Yamai ta ce ta janye daga yarjejeniyar soji da ta kulla da Amurka.
Wallafawa ranar:
Rahotanni daga birnin na Yamai,na nuni cewa dalibai da wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatin soji na daga cikin mutanen da suka taru a gaban hedikwatar majalisar dokokin kasar da ke birnin Yamai.
Korar dakarun kasashen waje,ba wani sabon abu ba ne a Nijar, an kori sojojin Faransa a karshen shekarar 2023, yanzu haka kusan sojojin Amurka 1,000 ne suka kasance a garin Agadez da ke arewacin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu