Isa ga babban shafi

Sojojin Nijar 6 sun mutu a wani harin bam a yankin Inates da ke kusa da Mali

Rundunar sojin Nijar  a wata sanarwa ta bayyana mutuwar sojoji 6 sakamakon wani harin bam a kusa da Mali, an kai musu hari ta sama.Majiyar ta bayyana cewa sojojin sun dawo daga aikin  sintiri daga Inates’ bayan ta tsallake rijiya da baya a wata mahakar ma’adinan da ke kusa da kauyen Tingara dake kudu maso yammacin kasar.

Sojojin Nijar na sintiri a yankin Ayoru da ke arewa maso yammacin birnin Yamai.
Sojojin Nijar na sintiri a yankin Ayoru da ke arewa maso yammacin birnin Yamai. © ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Rundunar ta karasa da cewa wasu sojoji sun jikkata kuma an kwashe su da jirgi mai saukar ungulu zuwa asibitin birnin Yamai.

Ma'aikatar ta kara da cewa sa ido ta sama ya ba da damar "gano 'yan ta'adda uku da ke da hannu" a cikin wannan aiki ta’addanci.

Ta kara da cewa, "An bi su zuwa wani yanki" inda suka hada da "kusan wasu masu hannu da shuni guda ashirin" sannan kuma an kai harin ta sama, wanda ya basu damar kashe wasu ‘yan ta’addan tare da lalata tarin makamai.

Garin Intaes,inda Nijar ta yi asarar dakaru biyo bayan harin 'yan ta'adda a shekarar 2019
Garin Intaes,inda Nijar ta yi asarar dakaru biyo bayan harin 'yan ta'adda a shekarar 2019 RFI/Moussa Kaka

A cikin wannan tsari, an sake kai wani hari ta sama a kan "gungun 'yan ta'adda" a yankin Amalaoulaou na kasar Mali,hakan ya baiwa rundunar tsaron ta Nijar damar kashe ‘ ;yan ta’adda takwas.

Garin na Inates na cikin yankin Tillabéri, wanda ya zama maboyar mayakan masu ikirarin jihadi a yankin Sahel, ciki har da na kungiyar Da'esh a cikin babban yankin Sahara karkashin inuwar kungiyar  Al-Qaeda.

A watan Disambar 2020 a Inates, an kashe sojojin Nijar 71 a wani hari da aka kai sansaninsu, wanda kungiyar  Al-Qaeda ta dau alhaki.

Jami'an tsaro a wasu yankunan  da ake fuskantar matsalar tsaro a Tillabery
Jami'an tsaro a wasu yankunan da ake fuskantar matsalar tsaro a Tillabery RFI

Tun bayan fadawa karkashin ikon sojoji daga karshen watan Yulin 2023, kasar ta Nijar ke karkashin jagorancin sojoji da suka dau alkawali na ganin sun karfafa tsaro a karkashin hadin gwuiwar kungiyar AES da ta hada da Mali,Burkina Faso da kasar ta Nijar.

Shugaban mulkin sojin Nijar Abdourahmane Tchiani tare da mukarrrabansa a birnin Yamai
Shugaban mulkin sojin Nijar Abdourahmane Tchiani tare da mukarrrabansa a birnin Yamai © REUTERS/Balima Boureima/File Photo

Duk da wannan kokari,ita ma kasar Nijar na fuskantar kalubale, a yankinta na kudu maso gabashin ta da Najeriya,inda wasu kungiyoyi ke ci gaba da garkuwa da kuma kisan mutanen a kauyuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.