Isa ga babban shafi

Nijar da Mali da Burkina Faso sun kafa rundunar yaki da ta'addanci a Sahel

Kasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso sun sanar da kafa wata rundunar dakarun hadaka wadda za ta yi aikin yaki da matsalar ta’addancin da ke addbar kasashen 3 na yankin Sahel tsawon shekaru.

Wakilcin kasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso yayin wani taro a birnin Ougadougou.
Wakilcin kasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso yayin wani taro a birnin Ougadougou. AFP - FANNY NOARO-KABRE
Talla

Bayan sanarwowin bangarorin 3 da ke tabbatar da kafuwar rundunar a jiya Laraba, babban hafson Sojin Nijar Salaou Barmou bayan wata ganawa a birnin Yamai ya ce suna fatan faro aikin rundunar gadan-gadan nan gaba kadan.

Kasashen 3 wadanda dukkaninsu Sojoji ke mulkarsu bayan juyin mulki kuma suke da kyakkyawar alakar tsaro yanzu haka tsakaninsu da Rasha sun yi amannar hadakar za ta taimaka wajen dakile matsalolin tsaron da ke ci gaba da lakume dubunnan rayukan al’ummominsu.

Tsawon shekaru kenan kasashen na Nijar da Mali da kuma Burkina Faso na fama da matsalolin tsaro masu alaka da kungiyoyin da ke ikirarin jihadi da karfin tsiya, lamarin da ya kai ga juyin mulkin Soji sakamakon zargin gazawar gwamnatocin fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.