Isa ga babban shafi

Kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar sun yi watsi da sharuddan ECOWAS

Kasashen Burkina Faso, Mali da kuma Nijar sun yi watsi da sharadin ECOWAS na cika wa’adin shekara guda gabanin iya fita daga cikin kungiyar kamar yadda suka bukata kwanaki 10 da suka gabata.

Wara hadakar sojin da ke mulki a kasashen Mali da Nijar da kuma Burkina Faso.
Wara hadakar sojin da ke mulki a kasashen Mali da Nijar da kuma Burkina Faso. AP - Chinedu Asadu
Talla

Kasashen 3 wadanda suka mikawa ECOWAS bukatar ficewa daga cikinta a ranar 28 ga watan Janairun da ya gabata, cikin wasu mabanbantan sanarwar kowaccensu ta bayyana cewa ba ta da shirin bata lokaci gabanin ficewa daga cikin kungiyar ta yammacin Afrika.

Sadarar doka ta 91 karkashin yarjejeniyar ECOWAS ta zayyana cewa dole ne duk wata kasa da za ta fita daga cikinta sai ta shafe akalla shekara guda ta na bin dukkanin ka’idoji da tanade-tanaden kungiyar gabanin iya samun sukunin fita.

Sai dai kasashen 3 wadanda dukkaninsu Sojoji ke mulkarsu, wadanda kuma ke takun saka da kungiyar tun bayan kakaba musu takunkumai sun ce wasikar da suka aikewar kungiyar ita ke tabbatar da ficewarsu a hukumance.

Sanarwar da Mali ta aikewa ECOWAS ta ce kasar ba za ta mutunta bukatar t aba, kuma kai tsaye ta fice daga cikinta domin kuwa ita kanta kungiyar ba ta mutunta bukatar Bamako ba bayanda ta sanya kasashe suka kulle mata iyaka a 2022.

Haka zalika Burkina Faso ta aike da makamanciyar wasikar wadda ke nesantata da bukatar ta ECOWAS tare da bayyana kanta a matsayin kasar da ba mambar kungiyar ba, yayinda Nijar ma ta tabbatar da ficewarta daga cikin kungiyar a wasikarta ta makon jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.