Isa ga babban shafi

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 155 a Kenya

Firaministan Tanzania Kassim Majaliwa ya ce akalla mutane 155 suka rasa rayukansu a kasar, sakamakon mamakon ruwan sama da ake ganin ya haifar da ambaliyar ruwa da zamtarewar kasa.

Akalla mutane 155 suka rasa rayukansu a Kenya, sakamakon mamakon ruwan sama da ya haifar da ambaliyar ruwa da zamtarewar kasa.
Akalla mutane 155 suka rasa rayukansu a Kenya, sakamakon mamakon ruwan sama da ya haifar da ambaliyar ruwa da zamtarewar kasa. © Monicah Mwangi / REUTERS
Talla

Firaministan ya ce sama da iyalai dubu dari biyu ne ambaliyar ruwar ta shafa, daga cikin adadadin mutane 155 sun mutu wasu 236 sun samu raunuka.

A lokacin da yake yiwa majalisar dokokin kasar jawabi a Alhamis din nan, Majaliwa ya ce bayaga asarar rayuka da ambaliyar ruwan ta haifar, ta kuma lalata gidaje da amfanin gona da hanyoyi da gadoji da layin godo da dai sauransu.

Yankin Gabashin Afrika na daga cikin yankunan da ke fama da matsalar sauyin yanayi wanda ya haifar da mamakon ruwan sama a daminar bana, inda ya haifar da asarar rayuka a kasashe irinsu Kenya da Burundi.

Sama da mutane dubu 96 ne ambaliyar ruwa ta shafa a Burundi.
Sama da mutane dubu 96 ne ambaliyar ruwa ta shafa a Burundi. Uganda Red Cross Society

A Burundi, daya daga cin  matalauciyar kasa a duniya, kimanin mutane dubu 96 ne ambaliyar ruwan ta raba da gidajensu, daga cikin wancan adadi mutane 45 ne kuma aka tabbatar da mutuwarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.