Isa ga babban shafi

Ambaliyar ruwa ta kashe mutane 11 tare da lalata gidaje dubu 2 a Kenya

Fiye da mutane dubu 2 ne suka rasa matsunansu a yammacin Kenya bayan wata ambaliya da ta afkawa kasar wadda ta tsananta a jiya Alhamis, matakin da ya tilasta gwamnati shiga aikin fara kwashe al’ummomin yankunan da ke fuskantar barazana.

Wani yanki a Kenya da ke fama da ambaliyar ruwa.
Wani yanki a Kenya da ke fama da ambaliyar ruwa. REUTERS - STRINGER
Talla

Kafofin labaran kasar sun ce zuwa yanzu ambaliyar wadda aka dauki kwanaki ana gani gabanin tsanantar ta a baya-bayan na ta kashe mutane 11 baya ga rushe matsugunan wasu mutum dubu 2.

Tun gabanin tsanantar ambaliyar dama hukumar kula da yanayi ta Kenya ta yi hasashen kasar ta fuskanci kakkarfan ruwan sama a bana inda ta bukaci jama’a su kasance cikin shirin fuskantar ambaliyar ruwa.

A yankin Kirinyaga da ambaliyar ta fi tsananta bayanai sun ce ruwan ya dakatar da harkokin zirga-zirgar ababen hawa, yayinda ya ke ci gaba da illa ga titiuna.

Ko a talatar da ta gabata sai da jami’an agaji suka shiga aikin ceto fasinjan wata motar safa su 51 da ruwa ya yi awon gaba da su daga wata babbar gasa a yankin arewacin kasar ta Kenya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.