Isa ga babban shafi

Kenya ta kori likitoci 100 daga cikin masu yajin aikin neman karin albashi

Mahukuntan Kenya sun sanar da korar akalla likitoci 100 cikin wadanda ke yajin aikin kusan wata guda a sassan kasar, likitocin da ke bukatar kara musu albashi baya ga biyansu wasu hakkoki da gwamnatin kasar ta yi alkawarin biya ba kuma tare da cikawa ba tsawon shekaru.

Likitocin Kenya da ke yajin aiki don neman kyautata yanayin aikinsu.
Likitocin Kenya da ke yajin aiki don neman kyautata yanayin aikinsu. REUTERS - Monicah Mwangi
Talla

Babban asibitin jami’ar Kenyatta da ke birnin Nairobi ya sanar da korar likitocin da aiki a cikinsa 100 wadanda ya ce tuni aka dauki wasu aiki don maye gurbinsu bayanda suka shafe kusan wata guda ba tare da aiki ba.

Tun cikin watan Maris din da ya gabata ne, likitocin na Kenya suka tsunduma yajin aiki inda suke bukatar kara musu albashi da kuma kyautata yanayin aikinsu.

A Lahadin da ta gabata ne shugaba William Ruto ya kawo karshen gum da bakinsa game da yajin aikin likitocin, inda a wani jawabi da ya gabatar, ya bayyana cewa Kenya ba ta da kudin da za ta iya biyan likitocin abin da suke bukata.

A cewar Ruto kasar ba za ta iya ciyo bashi don biyan albashi ba, don haka akwai bukatar likitocin su fahimci halin da ake ciki su kuma gane cewa dole Kenya ta yi rayuwa da abin da ta ke samu kuma dai dai da karfinta.

Ko a Talatar da ta gabata, dubban likitocin na Kenya sun gudanar da wani gangami tare da neman majalisa ta shiga tsakani wajen tirsasa gwamnati biyansu hakkokinsu karkashin alkawarin da aka cimma a 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.