Isa ga babban shafi

Gwamnatin Kenya ta fusata dangane da kisan wasu giwaye a kasar domin fataucin haurensu

Gwmamnan gundumar Kajialo Joseph Ole Lenku, ya bayyana takaicinsa game da kisan wasu giwaye guda biyu da masu farautarsu domin cire musu haure suka yi a wani yanki na kasar dake da iyaka da Tanzaniya.

Tarin hauren giwa
Tarin hauren giwa REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Wani gwamna a Kenya ya nuna matukar damuwa dangane da mutuwar giwaye uku da aka samu sanadiyar masu farautar haure a makwabciyar kasar Tanzaniya, a cewar wata sanarwar da aka fitar ga manema labarai.

Gwamnan gundumar Kajiado, Joseph Ole Lenku, wanda ya hada da gandun dajin Amboseli, wanda ke kan iyaka da Tanzaniya, ya nuna matukar tashin hankalinsa a game da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan na farautar giwaye a bangaren Tanzaniya.

Yayin da yake tabbatar da "mutunta 'yancin kowace kasa", gwamnan ya jaddada cewa giwayen da ke tsallaka kan iyakokin kasashen biyu akai-akai, suna nuna alakar da ke tsakanin halittu ne da kuma shaida mahimmancin kiyaye iyakokin kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.