AU ta bukaci tashi tsaye wajen warware matsalar da ECOWAS ta shiga
Kungiyar Tarayyar Afirka AU ta bayyana matukar rashin jin dadi akan matakin da gwamnatocin sojin Burkina Faso da Mali da kuma Nijar suka dauka na ficewa daga cikin kungiyar ECOWAS ta yammacin nahiyar Afirka.
Wallafawa ranar:
Cikin sanarwar da ta fitar, AU ta ce shugaban hukumar gudanarwarta Moussa Faki Mahamat, yayi kira ga shugabannin kasashen ECOWAS da su tashi tsaye wajen tattaunawa da kasashen uku da suka shelanta ficewa daga cikinsu.
A ranar Lahadin da ta gabata Nijar da Mali da kuma Burkina Faso, suka sanar da matakinsu na ficewa daga cikin ECOWAS, bayan shafe watanni ba tare da kyakkyawar alaka tsakaninsu da kungiyar ba, saboda juyin mulkin da sojoji suka yi a cikinsu.
A watan Yulin bara ne dai sojojin Nijar suka yi juyin Mulki, na Burkina Faso kuma a shekarar 2022, yayin na Mali suka kawar da gwamnatin farar hula a 2020.
Wannan ce kuma ta sa duk da cewar kasashen uku jiga-jigai ne wajen kafa ECOWAS a shekarar 1975, hakan bai hana kungiyar daukar matakin ladabtarwa na kakaba musu takunkumai ba, domin tilasta wa sojojin kasashen mayar da Mulki ga farar hula.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu