Isa ga babban shafi
ECOWAS

Gowon ya bukaci ECOWAS da ta janyewa Nijar, Mali da Burkina takunkumi

Afirka – Tsohon shugaban Najeriya Janar Yakubu Gowon ya bukaci kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da su sake tunani a kan matsayin da suka dauka na ficewa daga kungiyar ECOWAS saboda illar da hakan ka iya haifarwa baki daya.

Tsohon Shugaban Najeriya Yakubu Gowon
Tsohon Shugaban Najeriya Yakubu Gowon RFI Hausa
Talla

Gowon wanda ke jawabi ga manema labarai a Abuja, ya bayyana matukar damuwar sa da matakin da ya janyo janyewar wadannan kasashe daga kungiyar wadda ke hada kai da kuma bunkasa tattalin arzikin yankin.

Tsohon shugaban ya kuma bukaci ECOWAS da ta janye takunkumin karya tattalin arzikin da ta kakabawa kasashen guda 3 sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a cikin su.

Gowon ya bukaci hawa teburin tattaunawa tsakanin bangarorin biyu da zummar samar da maslahar da zata biyo baya, ganin yadda takunkumin ke illa ga talakawan dake wadannan kasashe.

Janar  Abdourahamane Tiani
Janar Abdourahamane Tiani © ORTN

Janar Gowon ya jaddada muhimmancin ci gaba da hadin kai tsakanin daukacin kasashen dake yankin Afirka ta Yamma domin tinkarar dimbin matsalolin da suka addabe su.

Kungiyar ECOWAS ta dauki matakin ladabatar da wadannan kasashe ne saboda kifar da zababbun gwamnatocin da sojoji suka yi, matakin da ya kai ga sanya musu takunkumin karya tattalin arziki.

Duk yunkurin ECOWAS na lallashin sojojin da suka yi juyin mulki na gabatar da shirin mika mulki ga fararen hula ya ci tura, yayin da kungiyar ta samu goyan baya a kan matakan da take dauka daga kungiyar kasashen Afirka ta AU da kuma Majalisar dinkin duniya.

A karshen wannan mako ake saran shugabannin kungiyar ECOWAS su gudanar da wani taron gaggawa a Abuja domin nazari a kan halin da ake ciki a wadannan kasashe da sojoji suka yi juyin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.