Isa ga babban shafi

Wasu bakin haure 38 sun mutu a kan hanyar tafiya Yemen - IOM

Afirka – Hukumar dake kula da kaurar baki da duniya IOM, tace an gano gawarwakin baki 38 kusa da gabar ruwan kasar Djibouti, bayan da wani kwale kwalen dake dauke da su ya yi hadari.

Firaministan Habasha, Abiy Ahmed kenan.
Firaministan Habasha, Abiy Ahmed kenan. AP - Mulugeta Ayene
Talla

Hukumar tace cikin wadanda suka mutu harda kananan yara, yayin da wasu mutane 6 kuma aka bayyana cewar sun bata daga cikin matafiyan, kana 22 sun tsallake rijiya da baya, kuma ana kula da su a kasar Djibouti.

Ofishin jakadancin Habasha dake Djibouti yace an samu hadarin ne jiya litinin a cikin kwale kwalen mai dauke da mutane 60 da suka fito daga kasar su zuwa Yemen.

A kowacce shekara daruruwan baki 'yan Afirka kan yi irin wannan tafiya mai hadari zuwa kasashen Turai da kuma kasar Yemen a kan hanyar su ta zuwa Saudi Arabia domin samun aikin da zai fidda su daga talauci.

Ofishin jakadancin Habasha yace a kowacce shekara baki sama da dubu 200 ke barin gabar ruwan Aden daga Djibouti domin tafiya kasashen dake Gabas ta Tsakiya, yayin da a cikin shekaru 5 da suka gabata, 'yan kasar Habasha 189 suka mutu sakamakon irin wannan hadari.

Ofishin yace wadannan matasa na jefa kan su da iyalan su cikin mummunan hadari, saboda haka sun gargade su da su kaucewa yaudarar masu safarar mutane.

Ofishin hukumar dake kula da kauran baki ta IOM tace akalla baki kusan 1,000 suka mutu a kan wannan hanyar a cikin wannan shekarar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.