Isa ga babban shafi

An gano karin gawawwaki a dajin Shakahola na kasar Kenya

Hukumomi a kasar Kenya sun fitar da sanarwar cewa, adadin wadanda suka mutu a wani bincike da ake alakantawa da wata kungiyar asiri sakamakon azabtar da kai da tsananin yunwa don saduwa da Yesu Almasihu ya zarce 400 bayan an gano wasu karin gawarwaki a dajin Shakahola.

Goman gawawwakin da aka gano a kauyen Shakahola na kasar Kenya.
Goman gawawwakin da aka gano a kauyen Shakahola na kasar Kenya. AP
Talla

Adadin wadanda suka mutu ya kai 403, kamar yadda kwamishiniyar yankin gabar teku, Rhoda Onyancha ta shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP, biyo bayan binciken da aka yi a dajin Shakahola, inda ake zargin shugaban kungiyar Paul Nthenge Mackenzie ya bukaci mabiyansa da su kashe kan su ta hanyar yunwa.

Bisa ga binciken da gwamnatin kasar ta gudanar, ga dukkan alamu yunwa ce ta haddasa mace-mace, ko da yake akwai wadanda ake zargin an shake su ne ko kuma duka, cikinsu kuwa akwai kananan yara.

Mackenzie, wanda ya kasance tsohon direban tasi da ya koma mai bishara, yanzu haka yana hannun 'yan sanda tun tsakiyar watan Afrilu.

A ranar 3 ga watan Yuli wata kotu a birnin Mombasa ta tsawaita tsare shi da wata guda kafin a kammala bincike.

Masu shigar da kara na kasar sun ce yana fuskantar laifukan ta'addanci ko kuma kisan kare dangi.

An dai diga ayar tambaya game da yadda Mackenzie, wanda ya bayyana kansa a matsayin limamin coci, kuma mahaifin 'ya'ya bakwai, ya yi nasarar kaucewa tuhume-tuhume duk da tarihin tsattsauran ra'ayi da shari'o'in da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.