Isa ga babban shafi

Gwaje-gwaje sun nuna cewa babu wasu sassa a jikin gawarwakin da aka gano a Kenya

Binciken da aka y ikan gawawwakin da aka gano a cikin manyan kaburbura da ke da alaka da wata kungiyar asiri ta Kenya, ya nuna bacewar sassan jikinsu da kuma haifar da shakkun an tilasta musu aikata abin da bas u yi niyya ba, in ji masu binciken yayin da aka gano karin wasu gawawwaki 21.

Yadda jami'an tsaro ke neman gawawwakin da aka binne a dajin Shakahola na kasar Kenya
Yadda jami'an tsaro ke neman gawawwakin da aka binne a dajin Shakahola na kasar Kenya AP
Talla

Ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 133 a wani abin da ake kira kisan kiyashin dajin Shakahola tun bayan gano kaburbura a watan da ya gabata abin da ya girgiza kasar mai yawan mabiya addinin Kirista.

‘Yan sanda sun yi imanin cewa, akasarin gawarwakin da aka gano a kusa da Malindi da ke gabar tekun Indiya na Kenya, mabiyan wani fasto ne mai suna Paul Nthenge Mackenzie, wanda ake zargi da ba su umarnin kashe su da yunwa domin su gana da Yesu almasihu.

Yayin da ake ganin cewa yunwa ce ta haddasa mutuwar, wasu daga cikin wadanda abin ya shafa ciki har da yara ana zargin shake su aka yi, ko kuma an yi musu dukan tsiya, a cewar babban mai binciken kan gawawwakin Johansen Oduor.

Masu binciken sun ce sun yi imanin za a samu karin gawarwaki a cikin kwanaki masu zuwa.

Bayanan kotun da aka shigar a ranar Litinin sun ce an cire wasu sassa a jikin gawawwakin, inda ‘yan sanda ke zargin wadanda ake zargin na da hannu wajen safarar sassan jikin dan adam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.