Isa ga babban shafi

Ana ci gaba da lalubo dazukan da aka binne gawawwaki a Kenya

Masu bincike a Kenya sun ci gaba da neman 'yan kungiyar asiri a cikin dajin da aka tono gawarwaki sama da 100 galibi yara kanana, wadanda wani mummunan ibtila’i ya rutsa da su, in ji ministan harkokin cikin gida Kithure Kindiki.

Dajin Shakahola, da aka gano kaburburan daruruwan mutanen da suka mutu a kasar Kenya kenan.
Dajin Shakahola, da aka gano kaburburan daruruwan mutanen da suka mutu a kasar Kenya kenan. AFP - YASUYOSHI CHIBA
Talla

An tsare Paul Mackenzie, shugaban Cocin Good News International, wanda aka zarga da umartar mabiyansa su kashe kansu da kuma ’ya’yansu  ta hanyar yunwa don samun damar ganawa da Yesu Almasihu, wanda ya yi hasashen cewa hakan zai faru a ranar 15 ga watan Afrilu.

Yayin da ake tunanin bacewar daruruwan mutane, an dakatar da aikin bincike a dajin Shakahola da ke kudu maso gabashin Kenya na 'yan kwanaki saboda rashin kyawun yanayi amma yanzu an sake fara aiki, in ji Kindiki yayin wata ziyara.

Ya ce an gudanar da bincike a kan gawarwakin mutane 112 da aka tono ko kuma aka tsinto su daga Shakahola.

“Ana ci gaba da gudanar da bincike da ceto mutanen da ake zargin sun makale a cikin dazuka,” in ji ministan.

A ranar Juma’a ne shugaban kasar William Ruto ya sanar da gudanar da bincike kan yawan mace-macen, yayin da wata kotu ta ci gaba da tsare Mackenzie har sai an kammala bincike.

Har yanzu ba a bukaci Mackenzie ya shigar da kara kan duk wani tuhume-tuhumen da ake yi masa ba, haka zalika lauyoyi biyu da ke kare shi sun ki cewa komai game da tuhumar da ake masa.

A makon da ya gabata ne wata kotu ta bayar da belin Ezekiel Odero, wanda hukumomi suka ce suna da hannu a kisan gillar da aka yi wa mabiyansa.

Ba kamar na Mackenzie ba, 'yan sanda da hukumomi ba su ce komai ba game da gawarwakin da aka gano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.