Isa ga babban shafi

An sake gano gawarwakin masu gaggawar ganawa da Yesu a kasar Kenya

‘Yan sandan Kenya sun sanar da gano karin gawarwakin wasu mutane 26 mabiya wata kungiyar addini da ake zargin sun kashe kansu ne da kansu da yunwa bisa wata manufa tasu ta gaggawar haduwa da Yesu. 

‘Yan sandan Kenya sun sanar da gano karin gawarwakin wasu mutane 26 mabiya wata kungiyar addini da ake zargin sun kashe kansu ne da kansu da yunwa bisa wata manufa tasu ta gaggawar haduwa da Yesu.
‘Yan sandan Kenya sun sanar da gano karin gawarwakin wasu mutane 26 mabiya wata kungiyar addini da ake zargin sun kashe kansu ne da kansu da yunwa bisa wata manufa tasu ta gaggawar haduwa da Yesu. REUTERS - STRINGER
Talla

Tun a ranar asabar ce ‘Yan sandan suka sanar da gano gawarwaki 21 yayin da suka ce akwai hasashen adadin ka iya karuwa, yayin da a yanzu haka adadin gawawakin sun kai 47. 

Da farko dai anyi zargin mutanen sun kashe kansu ne da yunwa bisa amincewar cewa zasu zarce aljanna da zarar sun mutu ba tare da cin abinci ba, amma dai ana zargin suna da alaka da wata kungiya ta asiri. 

Shugaban tawagar jami’an tsaron da ke gudanar da bincike Charles Kamalu ya ce lamarin ya munana, ta yadda ake hasashen adadin ya karu. 

Ministan cikin gidan kasar Kithure Kindiki ya baiyana cewa na zagaye wani daji mai girman eka 800 tare da aiyana shi a matsayin wurin da ake aikata laifi.     

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.