Isa ga babban shafi

Masu azumin jiran ganawa da Yesu sun mutu a kasar Kenya

Akalla mutane 4 ne suka mutu a kasar Kenya yayin da wasu gommai suka tagayyara saboda azumin mutuwa da suke yi a wani mataki na gaggawar ganawa da Yesu almasihu. 

Wasu daga cikin  mabiya mujami'u masu zaman kan su a Kenya
Wasu daga cikin mabiya mujami'u masu zaman kan su a Kenya © Reuters
Talla

A wani gandun dajin lardin Kilifi da ke gabar tekun Kenya jami’an ‘Yan sanda suka tsinci gawar mutane hudu, yayin da aka kwantar da wasu 12 a wani asibitin. 

‘Yan sanda suka ce dandazon mabiya ne suka yi sansani a gandun dajin, inda suka kwashe kwanaki da dama babu ci babu sha wai suna azumin jiran Yesu Almasihu kamar yadda wani faston yankin ya bukaci su yi. 

Hukumomi suka ce sun ceto mutane 11 - shida daga cikin su sun tagayyara suna cikin mawuyacin hali a kokarin da suke yi na gaggauta mutuwar tsarki domin ganawa da Yesu. 

Wasu daga cikin mabiya addinin Kirista
Wasu daga cikin mabiya addinin Kirista AP - Marco Ugarte

 ‘Yan sandan sun ce za su koma dajin a wannan Jumma’a domin ci gaba da neman karin wasu mutanen sakamakon rahotannin da ke cewa har yanzu wasu na cikin dajin suna jiran ganin tashin duniya, tare da gudanar da bincike kan wani kabari da suka gani a can. 

Wadan nan mutane na biyayye ne ga wani babban malamin cocin Good News International, wanda da ma jami’an tsaro na bibiyarsa saboda akidar sa na kira ga mabiyarsa da su rika mutuwa da yunwa domin isa sama da gaggawa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.