Isa ga babban shafi

'Yan sandan Kenya sun sake haramta zanga-zangar 'yan adawa kan tsadar rayuwa

Rundunar ‘yan sandan Kenya ta haramta zanga-zangar da ‘yan adawa suka shirya sake gudanarwa a gobe litinin bayan makamanciyarta a makon jiya da ta juye zuwa rikici tsakanin masu boren da jami’an tsaro.

Zanga-zangar makon jiya a Kenya da ta juye zuwa rikici.
Zanga-zangar makon jiya a Kenya da ta juye zuwa rikici. AP - Ben Curtis
Talla

Babban sufeton ‘yan sandan Kenya Japhet Koome ya shaidawa manema labarai yau lahadi cewa, hukumar ‘yan sanda ba ta amince da duk wani yunkurin gudanar da bore a gobe litinin ba.

A cewar babban sufeton na Kenya, za su baza jami’ansu akan manyan tituna don kame duk wani da ya yi yunkurin tayar da hankali a gobe litinin, lura da yadda bangaren adawar ya ja daaga wajen gudanar da haramtacciyar zanga-zangar.

Jagoran adawar Kenya Raila Odinga ya bukaci al’ummar kasar su fita zanga-zanga a ranakun gobe litinin da alhamis mai zuwa don nuna bacin ransu kan matsin rayuwar da suke fuskanta sakamakon tashin da farashin kayaki ke ci gaba da yi.

A makon jiya dai zanga-zangar ta juye zuwa tarzoma inda aka kame mutane fiye da 200 baya ga jikkata wasu da dama inda ‘yan sanda suka yi amfani da hayaki mai sanya hawaye da kuma ruwan zafi don tarwatsa dandazon jama’a.

Akalla mutum guda jami’an ‘yan sandan suka kashe a tarzomar ta makon jiya yayinda aka jikkata ‘yan sanda 31.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.