Isa ga babban shafi

Masana a Kenya sun soki shirin Ruto na bayar da bashin kwanaki 15 ga 'yan Kasar

Shugaban Kenya William Ruto ya sanar kaddamar da kaso na biyu na shirin tallafa wa marasa galihu da kudade domin gudanar da sana’o’i da ake kira ‘’The Hustler Fund’’.

Shugaba William Ruto na Kenya yayin kaddamar da sabon shirin bayar da tallafin bashin rukuni na 2.
Shugaba William Ruto na Kenya yayin kaddamar da sabon shirin bayar da tallafin bashin rukuni na 2. © citizen tv
Talla

Wannan dai na daya daga cikin alkawurran da shugaban ya yi wa al’ummar kasar a lokacin yakin neman zabensa, sai dai wa'adin da aka diba na mayar da bashin a kwanaki 15 shi ne ya tayar da hankalin jama'a musamman masana tattalin arziki da ke ganin babu tabbacin bashin ya iya amfanar da kowa.

Ken Gichinga, masanin tattalin arziki a cibiyar Mentoria da ke Nairobi, ya bayyana tsayin a matsayin wanda ke cike da sarkakiya yana mai cewa wadanda za su amfana da wannan shiri su ne ‘yan kasuwar da ke sarrafa kudade a kowace rana, daga nan kuma kudaden za su sake komawa a hannu kanana da matsakaitan masana’antu.

To amma duk da haka a cewar sa irin wadannan masana’antu ba wai za su rike kudaden a cikin asusun ba ne, sai dai kudin zai ci gaba da zagayawa a tsakaninsu.

A game da mafi yawan jama’a wadanda ba su da wata sana’ar yi, da wadanda ba su da komai sai albashi a karshen wata, lalle za su iya samun wannan rance, amma abin tambayar a cewar Ken Gichinga ta yaya za su sarrafa kudaden?

Masanin tattalin arzikin ya bayyana cewa babu ta yadda mutum zai iya samun rance, ya gudanar da wata harka ta kasuwanci da bashin, sannan kuma ya iya biya a cikin kwanaki 15 masu zuwa, wannan na nuni da cewa tabbas wasu za su ci riba yayin da wasu za su yi asara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.