Isa ga babban shafi

Kenya da Rwanda sun bukaci janyewar 'yan tawayen M23 daga gabashin Congo

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta da takwaransa na Rwanda Paul Kagame sun yi wata tattaunawa da ta bukaci gaggauta janyewar ‘yan tawayen M23 da ke ci gaba da mamaye yankuna a Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.

'Yan tawayen M23 a Congo.
'Yan tawayen M23 a Congo. AFP - GUERCHOM NDEBO
Talla

Shugabannin kasashen biyu sun amince cewa wajibi ne ‘yan tawayen na M23 su fice daga yankunan da suka kama a gabashin Congo.

A cewar Kenyatta wanda tuni ya aike da dakarunsa don taimakawa makwabciyar tasa yaki da matsalolin tsaron da suka dabaibayeta, akwai bukatar tsagaita wuta tsakanin dakarun na Congo da ‘yan tawayen na M23 a yakin da suke ci gaba da gwabzawa da juna.

Wannan mataki na zuwa a dai dai lokacin da ake ci gaba da samun karuwar matasan da ke shiga aikin sa kai a yankin na gabashin Congo na fatattakar ‘yan tawayen na M23.

Zuwa yanzu M23 ta kame yankuna da dama wanda ke matsayin bore na baya-bayan nan da suka yi tun bayan hare-harensu a shekarar 2012 da ya kai ga tagayyara dubunnan iyalai a sassan Congo.

Congo wadda kef ama da hare-haren ‘yan bindiga tsawon shekaru, barazanar ta M23 ta zamo kari kan matsalolin tsaron da suka dabaibaye kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.