Isa ga babban shafi

Dubban mutane ne suka tserewa yunwa daga Somalia zuwa Kenya - MDD

Yayin da fari ya mamaye yankin kuryar gabashin Afirka, dubun dubatar 'yan Somaliya ne ke tsallakawa zuwa Kenya domin neman ruwa da abinci ga iyalansu.

Sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya kenan da ke kasar Kenya
Sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a duniya kenan da ke kasar Kenya © UNHRC
Talla

A cewar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, sama da ‘yan Somaliya dubu 80 ne suka isa Kenya a cikin shekaru biyu da suka gabata, domin gujewa rikice rikice da fari.

Da yawa wadanda tuni aka tilastawa tserewa saboda tashe-tashen hankula, masana suka ce fari shine babban dalilin da ya sanya su ficewa domin neman mafita.

Kusan mutane miliyan 1 suka rasa muhallansu a Somaliya, inda sama da 80,000 suka isa Kenya a cikin shekaru biyu da suka wuce, domin gujewa mummunan farin da ya aukawa kasar da ke kuryar gabashin Afirka.

Khadija Ahmed Osman mai shekaru 36 da haihuwa ta tsere daga garin Buale tare da 'ya'yanta takwas sannan ta isa Dadaab a watan Oktoba, inda ta yi watsi da kasuwancinta na otal yayin da yawancin mazauna garin suma suka tsere saboda tsananin fari.

A sansanin Dadaab, inda 'yan gudun hijirar Somaliya ke zaune sama da shekaru 30. Hussien Ibrahim Mohamed, yana cikin mutanen farko da suka fara zama a Dadaab a 1992. Kuma a halin ya kasance daga cikin mutanen da ke kokarin bakin ‘yan gudun hijira, musamman wajen tattara gudunmowa ga iyalai masu bukatar sutura, kudi ko kuma abinci.

Fiye da 'yan gudun hijirar Somaliya 50,000 da suka isa sansanin cikin 'yan shekarun nan na bukatar tallafi. MDD tana ba da taimako na yau da kullun tare da tallafawa 'yan Kenya da samar da ruwa da sauran agaji.

Kenya ta ba da kariyar kasa da kasa ga 'yan gudun hijira daga ko'ina cikin yankin, sama da shekaru talatin kuma a halin yanzu tana karbar 'yan gudun hijira sama da rabin miliyan da masu neman mafaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.