Isa ga babban shafi

Hukumomin Kenya sun haramta zanga-zangar yan adawa da aka shirya yi gobe litini

Hukumomin Kenya sun haramta zanga-zangar yan adawa dangane hauhawar farashin kayayyaki a Kenya,zanga-zangar da suka shirya yi a ranar litini bisa hujar cewa sun gaza cika wa'adin da doka ta kayyade na shigar da kara, in ji shugaban 'yan sandan Nairobi a ranar.

Wasu daga cikin masu zanga-zanga a kasar Kenya
Wasu daga cikin masu zanga-zanga a kasar Kenya REUTERS - MONICAH MWANGI
Talla

Raila Odinga, shugaban jam'iyyar Azimio la Umoja, ya ci gaba da ikirarin cewa zaben shugaban kasa na ranar 9 ga watan Agustan 2022 "an tafka magudi", kuma gwamnatin William Ruto ba ta da tushe.

Raila  Odinga ya yi kira da a gudanar da zanga-zanga a ranar litinin domin nuna adawa da hauhawar farashin kayayyaki da suka tashi a watan Fabrairu sama da shekara guda zuwa kashi 9.2% a kasar dake gabashin Afirka.

Dan adawar kasar Kenya Raila Odinga
Dan adawar kasar Kenya Raila Odinga REUTERS - MONICAH MWANGI

"Mun sami buƙatu biyu da suka iso da yammacin jiya da safiyar yau, ɗaya daga Azimio la Umoja ɗaya Kenya, ɗayan kuma daga ƙungiyar 'yan kasuwan Nairobi. Dukansu ƙungiyoyin sun yi niyyar shirya zanga-zangar lumana.

Sanarwar daga yan siyasar na zuwa ne bayan da Adamson Bungei, babban jami'in 'yan sanda na babban birnin kasar Kenya, ya bayyana cewa,yan adawa ba su  mutunta wa'adin kwanaki uku na gabatar da bukatar zanga-zangar.

Masu shirya taron sun shirya yin tattaki zuwa gidan gwamnati, fadar shugaban kasa.

Jagoran yan adawa Raila Odinga ya karasa da cewa "Gobe 20 ga Maris, ina son 'yan Kenya su fito da yawa, su nuna rashin gamsuwarsu da abin da ke faruwa a kasarmu,".

Shugaban kasar William Ruto ya shaidawa wata coci a Kapsabet da ke yankin Rift Valley inda ya bukaci Raila Odinga da ya dauki matakin da ya dace da doka da tsarin mulki, "Ba za ku yi mana barazana ba, da hargitsi.

Bisa sakamakon da hukumar zaben ta fitar, Raila Odinga ya sha kaye a hannun William Ruto da kusan kuri'u 233,000.

Bayan sanar da sakamakon a hukumance a watan Agusta, Raila Odinga, wanda ke fafatawa a karo na biyar a shugaban kasar, ya yi magana kan magudi tare da yin watsi da sakamakon.

Sai dai kuma an yi watsi da daukaka karar da ya shigar gaban kotun kolin kasar, inda mambobin kotun suka kada kuri'ar amincewa da William Ruto, inda suka gano cewa babu wata shaida da ke tabbatar da zargin Raila Odinga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.