Isa ga babban shafi

Wani dan kasar Kenya ya mutu bayan fadowa daga saman filin wasan Qatar

Wani dan kasar kasar Kenya, ya mutu bayan da ya fado daga saman ginin filin wasan na Lusail da ke kasar Qatar.

Daya daga cikin filayen wasannin da aka karbi bakwacin gasar neman cin kofin duniya a Qatar na Lusail dake Doha.
Daya daga cikin filayen wasannin da aka karbi bakwacin gasar neman cin kofin duniya a Qatar na Lusail dake Doha. REUTERS - KAI PFAFFENBACH
Talla

Qatar dake karban bakwancin Gasar neman cin kofin duniya ta sanar da soma bincike kan mutuwar John Njau Kibue mai shekara 24.

Bayanai sun ce matashin ya ji rauni sosai sakamakon fadowar da ya yi daga saman ginin a ranar Asabar, jim kadan bayan da kasar Argentina ta lallasa Croatia a wasan kusa da karshe na kofin duniya.

Rahotanni daga yankin sun ce, jami’an ba da agajin gaggawa ne suka fara duba John bayan faruwar hatsarin, kafin daga bisani aka dauke shi zuwa Asibitin Hamad inda a nan rai ya yi halinsa a ranar Talata.

Masu shirya gasar sun ce sun sanar da ‘yan uwan marigayin kan halin da ake ciki, inda suka bada tabbacin za su mika duk wani hakkin sa ga ‘yan uwansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.