Benzema ya koma tsohon klob ɗinsa Real Madrid daga Al Ittihad domin jinya
Dan wasan gaba na Al Ittihad, Karim Benzema, ya koma filin atisayen Real Madrid.
Wallafawa ranar:
Masanin harkokin wasannin kwallon kafar nan Fabrizio Romano wanda ya tabbatar da hakan a daren Laraba, ya ce Benzema ya je can ne domin a yi masa karin gwaje-gwaje da kuma jinya kan sabon raunin da ya samu.
Itama ƙungiyar Al Ittihad ta ƙasar Saudiya ta tabbatar haka, tare da mika godiya ga Real Madrid saboda taimakon da suka bayar wajen jinyar Benzema.
A wani mataki na bazata ne Karim Benzema ya bar Real ne ya koma Al Ittihad kyauta a bazara.
Kulob din na Saudiyya na sa ran dan wasan na Faransa ya iya buga wasanni biyar da suka rage a kakar wasa ta bana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu