Isa ga babban shafi

Benzema ya kafa tarihi a gasar cin kofin duniya ta kungiyoyi

Karim Benzema ya kafa tarihin zama dan wasa na farko da ya zura kwallo a wasannin cin kofin duniya na kungiyoyi wato Club World Cup har guda 4 bayan nasarar kungiyarsa ta Al-Ittihad da ta doke Auckland City da kwallaye 3 da nema a jiya.

Karim Benzema a kungiyarsa ta Al-Ittihad da ke taka leda a gasar lig din Saudiya.
Karim Benzema a kungiyarsa ta Al-Ittihad da ke taka leda a gasar lig din Saudiya. AFP - -
Talla

A minti na 40 ne Benzema ya zura kwallon ta jiya da taimakon Al Shanqiti bayan tun farko Romarinho de Silva da Kante sun zura kwallaye 2 a minti na 29 da 34.

Wasan na jiya na nuna cewa Benzema mai shekaru 35 ya haska a wasannin na gasar cin kofin duniya na kungiyoyi har sau 6 a tarihi, lura da yadda ya doka 5 da Real Madrid.

Haka zalika dan wasan na Faransa, ya yi nasarar lashe kofin har sau 5 a shekarun 2014 da 2016 da 2017 da 2018 da kuma 2022.

Al-Ittihad mai rike da kambun Saudi Pro League na wakiltar kasar ne a wannan gasa kuma a wasanta zagaye na biyu kai tsaye za ta hadu da Al Ahly daga wakilcin kungiyoyin Afrika.

A nan gaba ne Manchester City mai rike da kambun zakarun Turai za ta shigo gasar a matakin wasannin gab da na kusa da na karshe.

Auckland City dai na wakiltar kasashen yankin Oceania ne a gasar, sai dai kuma ta fara da kafar hagu lura da yadda aka zura mata kwallaye har 3 a mintuna 11 na farkon bude wasa.

Nasarar ta Al-Ittihad ce ta bata damar iya haduwa da Al Ahly ta Masar a Juma’a mai zuwa.

Sauran kungiyoyin da za su haska a wannan gasa sun hada da Fluminense da Manchester City da kuma Urawa Red Diamonds da sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.