Isa ga babban shafi

Qatar 2022: Argentina da Croatia sun shirya yi karon batta

Bayan makonni 3 na waanni masu armashi, a tsakanin tawaga daga kasashe 32, yanzu kasashe 4 ne suka rage a gasar kofin duniya da ke gudana a Qatar.

Messi da Modric za su fafata a matakin kusa da karshe na gasar kofin duniya da ke gudana a Qatar.
Messi da Modric za su fafata a matakin kusa da karshe na gasar kofin duniya da ke gudana a Qatar. © AFP
Talla

Lionel Messi da Argentina za su fafata da Croatia da Luka Modric a wasan kusa da karshe a yau Talata, kafin zakarun gasar a 2018, wato Faransa su yi karon batta da Morocco masu taka wa manya birki a gobe Laraba.

A filin wasa Lusail, Messi zai yunkura a karo na biyu cikin shekaru 8 don ganin yaa ci wannan koffi da yake matukar yunwarsa.

Sai dai  an caccaki tawagar Argentina a abin da aka kira rashin dattatu da suka nuna bayan  wasan da suka doke Netherlands, inda suka yi ta tsokanar abokan hamayyarsu nasu.

Kocin Argentina Lionel Scaloni ya yi watsi da zargin, inda ya zake cewa babu wata afuwa da ‘yan wasansa za su nema.

Masu caccakar sun ce ko Messi da ake girmamawa shine ma kan gaba a wannan abin da suka kira rashin dattaku.

Anjima a Talatar nan ce za a yi fafatawa da ake kyautata zaton za ta yi armashi a tsaknin Argentina mai Messi, da Croatia mai Modric.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.