Qatar 2022: Messi da Alvarez sun kai Argentina zagayen karshe
Argentina ta doke Croatia da ci 3-0 a gasar cin kofin duniya, nasarar da bata damar zuwa wasan karshe.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yanzu haka dai, kasar za ta kara da Faransa ko kuma Morocco a zagayen karshe na gasar.
Messi ya zura kwallonsa ta biyar a gasar da aka fara a kasar Qatar a bugun finariti, inda Julian Alvarez ya zura ta biyu a zagayen farko, daga bisanu ya zura ta ukun bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.
Messi, mai shekaru 35, wanda kasarsa ta sha kaye a hannun Jamus a wasan karshe na shekarar 2014, yana da burin lashe gasar cin kofin duniya na farko a tarihinsa.
Argentina dai na neman kofin na duniya karo na uku, bayan samun damar lashe gasar a 1978 da 1986.
Croatia wadda ta zo ta biyu a Rasha shekaru hudu da suka wuce, ta gaza samun dama daga ‘yan wasan gaba, inda ‘yan wasan tsakiya ne ke kokarin bada gudun mowa a wasan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu