Isa ga babban shafi

An tono gawarwaki 21 a Kenya a wani bincike da ake yi kan wata kungiyar asiri

An tono gawarwaki 21 a Kenya a wani bincike da ake yi kan wata kungiyar asiri da ake kyautata zaton mabiyanta sun kashe kansu da yunwa, kamar yadda majiyar ‘yan sanda ta bayyana a yau asabar, tana mai gargadin adadin na iya karuwa.

'Yan sandan kasar Kenya.
'Yan sandan kasar Kenya. © REUTERS/Baz Ratner
Talla

Hulumar tsro ta bayyana cewa a dunkule tun ranar asabar, suna da gawarwaki 21,” wata majiyar ‘yan sanda ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP da sharadin sakaya sunanta, yayin da take magana kan binne gawawwakin da aka yi a dajin Shakahola da ke gabashin Kenya.

Dakarun kasar Kenya
Dakarun kasar Kenya AP - Ben Curtis

Majiyar ta kara da cewa, "Ba su ma tankwasa saman ba wanda ya ba da wata alama ta karara cewa za su iya samun karin gawarwaki a karshen wannan bincike."

Wata majiyar ‘yan sanda ta tabbatar da adadin wadanda suka mutu, wanda kuma bisa sharadin sakaya sunansa..

Akalla yara uku na daga cikin wadanda abin ya shafa, in ji wata majiyar ‘yan sanda.

Nthenge, shugaban Cocin Good News International, ya mika kansa ga ‘yan sanda kuma an gurfanar da shi a watan jiya, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka bayyana, bayan da wasu yara biyu suka mutu da yunwa a hannun iyayensu.

Daga baya an sake shi bisa belin shilling na Kenya 100,000 kwatankwacin dalar Amurka 700.

‘Yan sanda sun ba da rahoton kama shi a ranar 15 ga Afrilu bayan gano gawarwakin mabiya hudu wadanda aka ce ya ce su kashe kansu da yunwa domin su hadu da Yesu.

‘Yan sandan Kenya sun ce a ranar Juma’a sun tono wasu gawarwaki uku.

Wasu mabiya cocin 11 -- mafi ƙanƙanta 17 kawai -- an kai su asibiti, uku daga cikinsu na cikin mawuyacin hali, bayan an ceto su a ranar 14 ga Afrilu.

'Yan sanda sun kai samame dajin ne bayan samun bayanan wadanda suka mutu a kan "jahilai 'yan kasar da ke fama da yunwa a karkashin sunan sun hadu da Yesu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.