Isa ga babban shafi

An bayar da belin limamin cocin da ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane a Kenya

An bayar da belin limamin majami’ar da ake zargi da yin sanadin mutuwar daruruwan mutane a Kenya, bayan ya gurfana a gaban kotu, sakamakon gano daruruwar kaburbura da aka yi a watan da ya gabata.

Ezekiel Odero
Ezekiel Odero REUTERS - STRINGER
Talla

Ezekiel Odero, hamshakin attajirin mai bishara a gidan Talabijin da ke alfahari da dimbin magoya bayansa, ana bincikensa ne kan wasu tuhume-tuhume da suka hada da kisan kai, garkuwa da mutane, tsatsauran ra'ayi, laifuffukan cin zarafin bil'adama, zaluntar yara, zamba da kuma karkatar da kudade.

Masu gabatar da kara na zargin Odero da alaka da shugaban kungiyar asiri Paul Nthenge Mackenzie, wanda ake tsare da shi yana fuskantar tuhumar ta’addanci kan mutuwar mutane sama da 100, wadanda yawancinsu yara ne, a wani abin da aka yi wa lakabi da kisan gillar dajin Shakahola.

Ana zargin Mackenzie, shugaban Cocin Good News International, da ingiza mabiyansa su kashe kan su ta hanyar yunwa domin su hadu da Yesu lamarin da ya girgiza al’ummar Kenya matuka.

‘Yan sanda sun nemi a tsare Odero, wanda aka fi sani da Fasto Ezekiel, na tsawon kwanaki 30 don kammala bincike.

Sai dai alkalin kotun mai shari’a Joe Omido ya bayar da umarnin a sake shi a kan kudin kasar shillings miliyan 1.5 na kasar Kenya kimanin dala 11,000, yana mai cewa zai ci gaba da ziyartar ofishina ‘yan sanda sau daya a mako.

Magoya bayan Odero sun yi shagulgula da wake-wake, raye-raye: suna mai cewa addu’a ce ta fito da shi, ba maita ba.

'Yan sandan Kenya sun kama Odero a ranar Alhamis din da ta gabata kan mutuwar mabiyansa tare da rufe Cocinsa da ke kudancin garin Malindi a gabar teku.

Ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 109 a dajin Shakahola, kuma yawancinsu kananan yara ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.