Isa ga babban shafi

An sake samun wani faston da mabiyansa ke mutuwa a Kenya

Hukumar 'yan sanda a Kenya ta kara kama wani fasto da shi ma ake tuhumarsa da aikata hannu a mutuwar mabiayansa a garin Muveni na gundumar Kifili da ke lardin Coast. 

Hankalin gwamnatin Kenya ya tashi yayin da ake ci gaba da samun karin gawarwaki a dajin Shakahola.
Hankalin gwamnatin Kenya ya tashi yayin da ake ci gaba da samun karin gawarwaki a dajin Shakahola. AP
Talla

Jaridar The Nation na kasar ta ruwaito Shugabar lardin, Rhoda Onyancha, yayin da ta ke yi wa manema labarai karin haske bayan kama shi a ranar Alhamis, ta ce Fasto Ezikel Odero na hannun jami'an 'yan sanda a hedikwatarsu da ke birnin Mombasa kuma zai fuskanci tuhume-tuhume da dama ciki har da na kashe mabiyansa.

 "Mun kama Fasto Ezekiel ne bisa zargin da ake yi masa kan yawa  mace-macen da ake yi a harabar majami'arsa kamar yadda jama'a suka sanar da mu".  In ji Shugabar.  

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin tsaron Kenya ke shan suka kan zargin yin sakaci wurin barin ayyukan wasu matsafa da ya yi haifar da mutuwar kusan mutum 100 a kauyen Shakahola. 

A wannan makon ne 'yan Majalisar Kenya suka umarci Sufeto Janar na 'yan sandan kasar da sauran shugabannin tsaro su yi wa 'yan kasa bayanin yadda aka jima ana aikata irin wannan miyagun laifuffuka ba tare da gwamnati ta sani ba. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.